Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin karkatar da kuɗaɗe a lokacin gwamnatinsa.
Jami’an EFCC sun bayyana cewa suna yi masa tambayoyi dangane da zarge-zargen da ake masa.
Sai dai wasu rahotanni na cewa Yahaya Bello ya je ofishin EFCC ɗin ne da kansa ba kamo shi aka yi ba.
Idan ba a manta ba Yahaya Bello, ya shiga wasan ɓuya tsakaninsa da EFCC tun bayan da ya sauka daga mulki.
Duk da zarge-zargen da EFCC ke masa na karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake mulkin Jihar Kogi, Bello ya musanta aikata hakan.