Hukumar PSC ta ɗaga likafar AIG Muhammad Usaini Gumel zuwa DIG.

Hukumar kula da aiyukan ƴan sanda ta kasa (PSC) ta yi ƙarin girma ga mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya, AIG Muhammad Usaini Gumel, daga AIG zuwa mukaddashin babban sufeton ƴan sanda DIG .

Kafin ɗaga likafar tasa, DIG M.U Gumel, shi yake jagorantar sashen aikin tsaro da al’umma dake Sashen Bincike da tsare-tsare na helkwatar rundunar ƴan sandan Najeriya a Abuja.

Haka zalika ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ƴan sandan jihohin Sokoto da Kano.

A lokacin da yake riƙe da muƙamin kwamishinan ƴan sanda, a jihar Kano, a ƙalla ƴan daba sama da 600 ne suka tuba tare ajiya makamansu , inda aka sauya mu su tunani tare da basu sana’o’in dogaro da kai.

Gumel ya bayar da muhimmiyar gudunmawar ɗorewar zaman lafiya, a zaɓen gwamna na shekarar 2023 dake jihar Kano tare da kuma nasarar da ya samu wajen rage aikata laifuka a faɗin jihar.

Sauran wadanda suka samu ƙarin girman sun haɗa da, mataimakan sufeton yan sandan Nijeriya 7, CP 13 , DCP 30, ACP 51, CSP 542, SP 119 da DSP 12.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *