Rahotannin na nuni da cewa har zuwa wannan lokaci hukumomin ƙasar Nijar ba su kai ga buɗe iyakokinsu ba duk kuwa da umarnin da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayar, a ranar 13 ga watan Maris na wannan shekara, na janye takunkumin da aka ƙaƙaba wa Nijar.
Tun bayan umarnin na shugaban ƙasa ne, shugabar hukumar shigi da fici ta ƙasa, Kemi Nandap, ta ba wa jami’an hukumar da ke jihohi da kuma iyakokin ƙasar nan umarnin buɗe iyakokin.
A baya dai shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka, ECOWAS wanda kuma sanar da ƙaƙaba wa Nijar takunkumai saboda kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da sojojin suka yi.
Sai dai kuma rahotannin sun tabbatar da cewa har yanzu hukumomin ƙasar Nijar ba su kai ga buɗe iyakokin da suke garuruwan Sokoto da ake bi ta Kebbi da Katsina da Jigawa da Yobe da kuma Borno ba.