Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa janye tsarin tallafin man fetur da kuma fatali da bambanci wajen farashin kudin ƙasashen ƙetare.
Sanusi II ya bayyana matsayarsa ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Mai girma shugaban kasa a jiya Alhamis.
Muhammadu Sanusi ya bayyana shugaba Tinubu a matsayin abokinsa wanda ya ce ya kama hanyar gyara kasa, wanda a dalilin hakan ne ma ya kawo masa ziyara.
Dayake bayani, Sunusi Lamido yace, kamar yadda aka san abubuwan da su ke magana a kai: tallafin man fetur ya zama ala-ƙa-ƙai, haka ma bambancin farashin kudin kasar waje da sauransu.
Ya ƙara da cewar, wadannan su ne abubuwan da ya ke magana a kai na tsawon lokaci, kuma ya yi farin ciki da shugaban ƙasa ya taɓo su.