Home » INEC Ta Fitar da Ranakun Miƙa Shaida Ga Zaɓaɓɓun Gwamnoni

INEC Ta Fitar da Ranakun Miƙa Shaida Ga Zaɓaɓɓun Gwamnoni

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohin ƙasar da aka gudanar da zaɓen gwamna.

A wata sanarwar da hukumar INEC din ta fitar mai ɗauke da sa- hannun shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu kada ƙuri’a na hukumar Festu Okoye, ta ce sashe na 72 (1) na dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun ‘yan takara a cikin kwana 14 da yin zaɓen.

A kan haka ne hukumar ta ce ta saka ranar Laraba 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan na Maris a matsayin ranar da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma ‘yan majalisun dokokin jihohi.

Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaɓen ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar.

Hukumar zaɓen ta ce kwamishinonin INEC na jihohi da ma’aikatan hukumar za su sanar da zaɓaɓɓun takamammiyar ranar da za su karɓi takardun shaida

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?