• Home  
  • INEC Ta Saka Ranar Fara Rajistar Masu Zaɓe A Faɗin Najeriya
- Babban Labari - Labarai

INEC Ta Saka Ranar Fara Rajistar Masu Zaɓe A Faɗin Najeriya

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027. Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki. […]

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.

Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.

Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.

INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma’a.

Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.

Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai