• Home  
  • INEC ta sanar da ranar fara karɓar katin zaɓe na PVC a faɗin Najeriya
- Babban Labari

INEC ta sanar da ranar fara karɓar katin zaɓe na PVC a faɗin Najeriya

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, ta ce za a fara rabawa da kuma karɓar katunan zaɓe na dindindin, PVC, daga ranar 9 ga Oktoba, 2026 a faɗin ƙasar. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Kaduna, yayin taron tattaunawa na shiyyar Arewa maso Yamma da ma’aikatan […]

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, ta ce za a fara rabawa da kuma karɓar katunan zaɓe na dindindin, PVC, daga ranar 9 ga Oktoba, 2026 a faɗin ƙasar.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Kaduna, yayin taron tattaunawa na shiyyar Arewa maso Yamma da ma’aikatan hukumar, tare da tantance matakin shirin da aka ɗauka gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Farfesa Amupitan ya ce aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a na baya-bayan nan ya samar da sabbin rajista sama da miliyan 10.7.

Ya yi kira da a kawar da matsalolin da ke kawo cikas ga rabon katunan a matakin ƙananan hukumomi, domin kauce wa hana ’yan ƙasa da suka cancanta cin moriyar haƙƙinsu na zaɓe.

Haka kuma, ya bayyana cewa INEC na inganta tsare-tsarenta na fasaha, ciki har da hanyoyin tantance masu kaɗa ƙuri’a da isar da sakamakon zaɓe, da kuma tsarin ƙirga sakamakon zaɓe, ciki har da sabon tsarin eEC8A da aka ƙaddamar.

Shugaban hukumar ya ce INEC na kuma aiwatar da tsarin ‘Zero-Failure’, wato manufar rashin samun tangarda a harkokin jigilar kayayyakin zaɓe.

Ya ce tsarin ya haɗa da kai kayan zaɓe tun da wuri, jigilar su, haɗin gwiwa da jami’an tsaro, da kuma horas da ma’aikatan wucin gadi da za a ɗauka domin gudanar da zaɓen.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai