Al’ummar garuruwa 11 da ke kewaye da Dam din Warwade a Jihar Jigawa, sun bayyana farin ciki na farfadowar tattalin arzikinsu, biyo bayan shirin farfado da dam din domin inganta noman rani da ƙara yawan amfanin gona da rage talauci a yankunan.
Manoman yankunan sun bayyana cewa, tsawon shekaru suna fuskantar kalubale wajen gudanar da ayyukan noma sakamakon raguwar ruwa a dam din da kuma lalacewar wasu kayayyakin aikin ban-ruwa, amma yanzu suna ganin shirin da Bankin Duniya ke tallafawa zai zama wata hanya ta farfado da sana’arsu da inganta rayuwarsu.
Sun bayyana hakan ne yayin bikin kaddamarwa da horar da mambobin Kwamitin Karbar da Magance Korafe-korafe na matakin jiha, tare da kafa kwamitocin matakin al’umma domin shirin noman ban-ruwa na Warwade karƙashin shirin Sustainable Power and Irrigation for Nigeria (SPIN).
Shirin na da manufar samar da ingantacciyar hanya mai saukin amfani, gaskiya da rikon amana wajen karbar korafe-korafe, rubuta su, bincike da kuma magance matsalolin da ka iya tasowa yayin aiwatar da ayyukan shirin.
Da yake jawabi a madadin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhammad Al-Hassan, Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Kasa, Injiniya Zayyanu Rabi’u, ya ce, zabar Jihar Jigawa cikin jihohin da za su ci gajiyar shirin ya biyo bayan kokari da jajircewar gwamnatin jihar wajen bunkasa harkokin noman ban-ruwa.
Ya bayyana cewa, Bankin Duniya ya tsara wasu sharudda da jihohi suka wajaba su cika kafin shiga cikin shirin, musamman nuna kuduri da shirye-shiryen zuba jari wajen bunkasa harkokin noman ban-ruwa.
A cewarsa, Jigawa ta nuna irin wannan kuduri ta hanyar shirye-shiryen da ta gabatar da kuma karin wuraren da take son shirin ya shafa, domin fadada amfaninsa ga al’ummar jihar.
Injiniya Zayyanu ya ce, kaddamar da kwamitocin karbar korafe-korafe zai taimaka wajen tabbatar da cewa, al’umma sun mallaki shirin a matsayin nasu, tare da daukar alhakin ci gaba da gudanar da ayyukansa bayan kammala tallafin Bankin Duniya.
Ya bukaci manoma da sauran al’umma da su ba da gudummawa wajen kare kayayyakin aikin, tare da tabbatar da dorewar shirin domin ya zama sanadin samun wadataccen abinci, bunkasar tattalin arziki da rage talauci.
Shi ma a nasa jawabin, Kodinetan shirin SPIN a Jigawa, Injiniya Alhassan Abbas, ya ce kaddamar da kwamitocin matakin jiha da na al’umma wani muhimmin mataki ne na tabbatar da shigar al’umma cikin gudanar da shirin.
Ya bayyana cewa, an kaddamar da kwamitin matakin jiha a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, yayin da aka kafa kwamitocin al’umma a Warwade da sauran garuruwan da ke amfana da ruwan dam din.
Ya ce, an samar da akwatunan sanya korafe-korafe da shawarwari a yankunan, inda jami’an kula da harkokin zamantakewa da jinsi za su riƙa zuwa lokaci-lokaci domin daukar saƙonnin da aka ajiye, tantance su da kuma daukar matakan da suka dace.
Injiniya Abbas ya yaba da irin hadin kan da al’ummar Warwade da garuruwan da ke makwabtaka da su suke bai wa shirin tun daga lokacin da aka fara hulda da su.
Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na da burin fadada noman ban-ruwa zuwa hekta 5,000 nan da shekarar 2030, yana mai cewa, Jigawa ma na kokarin taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri tare da goyon bayan Gwamna Malam Umar Namadi da shirin SPIN.
Tun da farko, Aisha Aminu, kwararriyar masaniya kan harkokin zamantakewa da kare hakkin, ta bayyana cewa, ƙaddamar da kwamitin matakin jiha zai taimaka wajen karba da rubutawa, tantancewa, bincike da tura korafe-korafe zuwa hukumomin da suka dace.
Ta ce, kwamitin zai kuma kula da korafe-korafen da suka wuce ƙarfin kwamitocin al’umma, domin tabbatar da cewa, an magance su cikin gaskiya da adalci.
A nata ɓangaren, Jami’ar kula da harkokin jinsi ta shirin SPIN, Hadiza Sabo, ta gabatar da bayani kan hanyoyin kare al’umma daga cin zarafi da kuma yadda za a taimaka wa wadanda abin ya shafa.
Ta bayyana cewa, cin zarafin da ya danganci jinsi ya hada da duka, fyade, cin zarafin lalata, barazana, wulakanci da hana mutum damar mallakar kasa, samun kudi, ruwa ko ilimi.
Ta ce, mata da ‘yan mata sun fi fuskantar irin wadannan matsaloli, duk da cewa maza da yara maza ma na iya zama waɗanda abin ya shafa.
Hadiza ta yi gargadin cewa, shigowar ‘yan kwangila, ma’aikatan kaura da sabbin hanyoyin samun kudi cikin al’umma na iya haifar da wasu hadurra na cin zarafi da muzguna wa mata idan ba a samar da ingantattun matakan kariya ba.
Ta jaddada muhimmancin sirrin bayanan wadanda abin ya shafa, kare su daga ramuwar gayya da kuma samar da hanyoyin kai rahoto zuwa hukumomin da suka dace domin samun taimako.
Horon ya kuma mayar da hankali kan wayar da kan mambobin kwamitocin, samar da hanyoyin tura korafe-korafe, haɗin kai tsakanin kwamitocin matakin al’umma da na jiha, da kuma tabbatar da cewa ana rubuta bayanan duk korafe-korafe domin sa ido da tantance ayyukan shirin.
A bangaren al’umma kuwa, wakilansu sun bayyana farin cikinsu da shirin, suna mai cewa farfado da Dam din Warwade zai taimaka wajen dawo da martabar noma da inganta rayuwar mazauna yankunan.
Aminu Musa Saya-Saya, ma’aji a wata kungiyar manoma, ya ce, a baya sun dade suna ƙoƙarin gudanar da ayyukan noma, amma ba sa samun sakamako mai kyau saboda raguwar ruwan dam ɗin.
Ya bayyana cewa, zuwan wannan shiri ya dawo musu da sabon fata na ganin an inganta harkokin noma tare da bunkasa tattalin arzikinsu.
Shi ma shugaban al’ummar Zuwan Hawa, Ali Garba, ya nuna godiyarsa ga masu gudanar da shirin, Bankin Duniya da Gwamnatin Jihar Jigawa bisa wannan kokari, yana mai fatan shirin zai amfani dukkan al’ummomin da ke kewaye da dam din.
Wata manomiya, Uwa Haruna Warwade, ta ce, mata sun yi farin ciki da shirin, inda ta tabbatar da cewa za su ci gaba da halartar duk wani taro ko shirin wayar da kan da za a gayyace su.
Haka kuma, wani wakilin matasa daga Warwade ya ce an daɗe da watsi da aikin dam ɗin, amma farfado da shi ta hanyar zamani zai taimaka wajen kawar da talauci, ba kawai a garuruwan da ke kewaye da shi ba, har ma da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.
Dam din Warwade na da alaka da garuruwa 11 da ke amfana da ruwansa, inda al’ummomin ke fatan fadada shi da inganta tsarin ban-ruwa domin kara samar da abinci, samar da guraben sana’a ga matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, kafa kwamitocin karbar korafe-korafe a matakin jiha da al’umma zai taimaka wajen karfafa hafin kan jama’a, tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da samar da hanyoyin magance matsalolin da ka iya tasowa yayin aiwatar da shirin SPIN
