• Home  
  • Gwamnatin Bauchi ta dakatar da sarkin Lame
- Labarai

Gwamnatin Bauchi ta dakatar da sarkin Lame

Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Sarkin Lame, Alhaji Yakubu Aliyu, kan zargin da ake yi masa da na karɓar haraji ba bisa ka’ida ba da kuma tsoma baki a harkokin filaye da kuma na haƙar ma’adanai. Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Bala Muhammad shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar […]

Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da Sarkin Lame, Alhaji Yakubu Aliyu, kan zargin da ake yi masa da na karɓar haraji ba bisa ka’ida ba da kuma tsoma baki a harkokin filaye da kuma na haƙar ma’adanai.

Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Bala Muhammad shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Asabar, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da wani kwamitin bincike mai mutum 12 da aka kafa zai kammala aikinsa.

Sanarwar ta ce an kafa kwamitin ne domin binciken sarkin kan zargin amfani da mukaminsa domin aikata ba daidai ba.

A cewar gwamnatin, ta samu korafe-korafe da dama da kuma rahotanni daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da kuma jami’an tsaro kan abubuwan da sarkin ke aikatawa.

Gwamnatin ta ce korafe-korafen sun haifar da damuwa a Masarautar Lame tare da tayar da hankalin al’umma da kuma hana zaman lafiya.

“Zarge-zargen da ake yi wa sarkin sun haɗa da saka baki a harkokin filaye, karɓar haraji ba bisa ka’ida ba da kuma katsalanda ga kamfanonin da ke haƙar ma’adinai,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa tun da farko Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya ta nemi Sarkin ya yi bayani kan zarge-zargen da ake yi masa, amma ya kasa kare kansa duk da cewa ya yi martani a rubuce.

Daga bisani ne ta yanke shawarar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa sarkin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000