Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa ta ce tana shirye-shiryen ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu wanda ta bai wa waɗanda suka shigar da ƙara damar yin zaɓe da katin zaɓe na wucin-gadi.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na tuwita, INEC ta ce;
“Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukunci wanda ya bai wa waɗanda suka shigar da ƙarar damar yin amfani da katin zaɓensu na wucin-gadi wajen kaɗa ƙuri’a.”
Sai dai bayanin ya ƙara da cewa Hukumar na duba matakan da suka kamata wajen ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
A ranar Alhamis ne mai shari’a Obiora Egwuatu ya bai wa masu shigar da ƙarar gaskiya, inda ya ce suna da ƴancin amfani da katunansu na wucin-gadi domin kaɗa ƙuri’a.
Mai shari’ar ya ce kotu ta yanke hukuncin bisa dogaro da cewa hukumar zaɓen na da bayanan mutanen, kasancewar sun riga sun yi rajistar katin zaɓe.
To amma dai INEC ta ce babu wanda zai kaɗa ƙuri’a har sai ya gabatar da katin zaɓensa na dindindin, tare da sharaɗin cewa an iya tantance shi ta hanyar na’ura.