Gwamnatin jihar kano ta ƙarya ta zargin da ake mata na kokarin kawo cikas akan shari’ar zargin kisa da ake wa Alasan Ado doguwa.
Gwamnatin, ta bakin babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a na jiha, Mai shari’a Musa Lawan ya bayyana haka ne a jiya juma’a a sai’lin da yake wa manema labarai jawabi
Kwamishinan yace duk da cewar an bayar da beli, hakan baya ya nuna cewar shari’a tazo karshe ba ne, amma dai ofishinsa bai samu takardar neman beli wanda ake zargi ba domin ba’a gabatar mata da ita ba.
Haka ya bayyana cewar jami’an yan sanda ne suka kawo musu takardun zargin da ake tuhumar shi Alasan doguwa a ranar Larabar da ta gabata a saboda haka suna bukatar lokaci domin su nazaarci kundin shai’ar domin abun yana bukatar nutsuwa duba da yanayin zarge-zargen da ke cikin shari’ar.
Kwamishinan ya ce sun duba takardun kuma ya bayar da umurnin mika kwafin takardun ga yan sanda a jiya alhamis inda ya ce bisa nazarinsu za su tuhumi wanda ake zargi a babban kotun jiha.
Ya kuma tabbatar da cewa za a yi shari’a bisa adalci ga ɓangaren masu ƙara da wanda ake kara