Iran ta ƙera wani sabon jirgi mara matuƙi mai suna Hadid 110, wanda aka ce yana tafiya da matsanancin sauri a ƙasa ƙasa, wanda ke iya kai farmaki cikin gaggawa kamar layar zana kafin na’urorin kariyar sararin samaniya su gano shi.
A cewar jaridar, an ƙera jirgin ne domin ya riƙa kutsawa ta cikin garkuwar kariyar sararin samaniyar Amurka ba tare da an gano shi cikin sauƙi ba.
Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce ta yi amfani da jirgin a karon farko wajen kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da kuma jiragen ruwanta da ke Gabas ta Tsakiya makonni biyu da suka gabata.
The Telegraph ta kuma ce an ƙera Hadid 110 ne domin maye gurbin tsohon jirgin Hadid, wanda Iran ke ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin muhimman makaman yaƙinta.
Rahoton ya ce babban abin da ya bambanta sabon jirgin da tsohon nau’in shi ne matuƙar gudunsa da kuma yadda yake iya kai hari ba tare da an gano shi da wuri ba.
An ƙera Hadid 110 ne domin ya kai hari kafin na’urorin kariyar sararin samaniya su gano shi ko su iya kakkaɓo shi, kamar yadda masana na Iran suka bayyana.
Jaridar ta ƙara da cewa an fara baje kolin jirgin a bara a gaban Jagoran Addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, kafin daga bisani a kashe shi a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila, kamar yadda rahoton The Telegraph ya bayyana.