Kasashen Ketare

Kenya ta hana taron jama’a saboda cutar Ebola

Ƙasar Kenya ta dakatar da gudanar da tarukan gwamnati da tarurruka a cikin otal-otal bayan ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola. Jami’an lafiya sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na dakile yaɗuwar cutar. A cewar hukumomi, mutumin da ya kamu da cutar, wanda ɗan […]

Read more

‘Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami’

Kim Yo Jong, ƴar’uwar shugaban Koriya ta Arewa kuma ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a gwamnatin ƙasar, ta bayyana cewa Pyongyang ta gudanar da gwajin makami mai linzami na dabarun yaƙi mai matsakaicin zango a safiyar ranar Asabar. Ta kuma ce ɗan’uwanta, shugaban ƙasar Kim Jong Un, da kansa ya halarta tare da sa […]

Read more

Gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium

Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin haƙar ma’adanai na Madaouela don sake fara aikin haƙar uranium, wani sabon mataki mai muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar. A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium. Ana sa ran yarjejeniyar za […]

Read more

Ebola ta ƙara bazuwa a DR Congo

Jami’ai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce barkewar cutar Ebola ta bazu zuwa wani lardi, wanda shi ne na bakwai. Gwamnan Sud-Ubangi ya ce an tabbatar da samun cutar a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Kongo. An yi imanin cewa majinyacin ya bi ta wasu larduna da dama, ciki […]

Read more

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da wata yarjejeniya ta sayar wa Saudiyya kayan makamai da darajarsu ta kai dala biliyan 5. A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta amince da buƙatar Saudiyya na sayen dubban bama-bamai da kuma na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango. A cewar […]

Read more

Nijar ta zargi Faransa ta kitsa juyin mulki a ƙasar

Hukumomin Nijar sun zargi Faransa a hukumance da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin “yunkurin kawo hargitsa ƙasar a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.” A cikin wata sanarwa, gwamnatin Nijar ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai, tana da “alaƙa da ƙasashen duniya”, […]

Read more