• Home  
  • ‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz
- Babban Labari

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz. Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman. UKMTO ta ce ma’aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin. A wani labarin na daban, wasu jiragen […]

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz.

Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman.

UKMTO ta ce ma’aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin.

A wani labarin na daban, wasu jiragen ruwan ƴan kasuwa biyu sun ce an kai musu hari yayin da suka yi yunƙurin wucewa ta mashigar, kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labari an Reuters.

Ɗazu ne dai rundunar sojin Iran ta sanar sake rufe mashigar Hormuz kwana guda bayan buɗe ta, saboda zargin Amurka da ci gaba da rufe tasoshin ruwan ƙasar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai