Jami’an Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS sun tsare Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, jim kadan bayan Shugaba Tinubu Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi.
Shugaban kasa Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele, daga aiki ba tare da bata lokaci ba, tare da ba da umarnin a bincike shi, ta wata sanarwar da Daraktan Yada Labarai, Willie Bassey ya fitar ta ce hakan ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishin Emefiele da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a fannin hada-hadar kudi da tattalin arzikin Najeriya.
An umarci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga mataimakinsa, wanda zai yi aiki a matsayin mukaddashin gwamnan babban banki.
A lokacin yakin neman zabe, Tinubu ya yi zargin cewa an bullo da sabbin tsare-tsaren kudin ne domin yi masa kafar ungulu, amma hakan ba zai hana shi yin nasara ba.
Emefiele ya nemi takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar APC amma Tinubu ya kayar da shi a zaben fidda gwani.