Home » Jami’ar Ahmadu Bello, ABU, Ta Sanar da Fara Zangon Karatu Na 2

Jami’ar Ahmadu Bello, ABU, Ta Sanar da Fara Zangon Karatu Na 2

by Anas Dansalma
0 comment
Jami'ar Ahmadu Bello, ABU, Ta Sanar da Fara Zangon Karatu Na 2

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta sanar da sake bude makarantar domin ci gaba da gudanar karatun zango na biyu.

A wata sanarwa da jami’ar ta fitar, ta ce sakamakon taron gaggawa karo na 523 da majalisar ta gudanar a jiya Juma’a 16 ga watan Yuni 2023,

 Rajotanni sun bayyana cewa daliban jami’ar sun shafe tsawon wata guda suna zaman gida sakamakon yanke wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna KEDCO ta yi a jami’ar.

Binciken da aka gudanar, ya tabbatar da dawowar wutar lantarkin, lamarin da ake zargin shi ne ya sa aka yi wa daliban kiranyen dawowa jami’ar.

Sai dai takardar sanarwar bata fayyace ko hukumar jami’ar ta samu nasarar biyan kudaden wutar lantarkin da ake binta ko kuma irin matsayar da suka samu da hukumar samar da wutar lantarkin don kaucewa faruwar irin haka a nan gaba.

Yanzu dai ana sa ran daukacin dalibai za su dawo a ranar Litinin don ci gaba da gudanar da karatu bisa tsarin yadda aka yi wa jadawalin karatun kwaskwarima.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi