Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya umarci Musulmai a faɗin Najeriya da su fara duban watan Zul-Hijja na shekrar 1444 ta hijira daga yau Lahadi.
Cikin wata sanarwa da kwamitin duban wata na ƙasar ya fitar mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu ta ce Sarkin Musulmin ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar.
Sanarwar ta ƙara da cewa watan Zul-Hijja na da muhimmanci kamar sauran watannin Musulunci, kuma shi ne na 12 cikin jerin watanni kalandar Musulunci, wanda a cikinsa ake yin ibadar aikin Hajji, tare da bikin Salla Babba.
Muna son sanar da duka Musulmi cewa ranar Lahadi 18 ga watan Yuni ita ce ta yi daidai da 29 ga watan Dhul Ƙa’ada, ita ce kuma ranar da ya kamata a fara neman watan Dhul Hijja cikinta na hijira ta 1444.” in ji sanarwar.