Jam’iyyar PDP ta ɗinke – Tanimu Turaki

Shugaban jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki ya ce yanzu jam’iyyar ta ɗinke ɓarakar da ta daɗe tana ciki, inda ya ce komai ya wuce a yanzu.

Turaki ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi, waɗanda ya ce sun kai masa ziyara ne domin taya tsaginsa murna tare da nuna mubaya’a kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Shugabannin jam’iyyar sun kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo, Tony Aziegbemi tare da wasu shugabannin jihohin guda 29.

A jawabinsa na maraba, ya buƙaci shugabannin na jihohi da su ba shi shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin jam’iyyar ta samu nasara, sannan ya yi watsi da iƙirarin tsagin Ministan Abuje Nyesom Wike cewa su ne asalin shugabannin jam’iyyar.

Ana dai ci gaba da fafatawa kan shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa, inda bayan tsagin Kabiru Turaki da ke samun goyon bayan Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, akwai kuma tsagin da ke samun goyon bayan Wike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *