Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi (FCA), ya ƙaddamar da Tsare-tsaren Bunƙasa Ƙananan Hukumomi (Local Government Development Plans-LGDPs) na shekarun 2025 zuwa 2030 ga ƙananan hukumomi 27 na jihar, inda ya bayyana matakin a matsayin wani babban tarihi da zai ƙarfafa shugabanci a matakin ƙasa, inganta ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da tsare-tsaren ci gaba masu dogaro da sahihan bayanai.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a zauren Majalisar Zartarwa da ke Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa a Dutse, tare da halartar mataimakin gwamna, kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, wakilan ƙungiyoyin farar hula da abokan hulɗar ci gaba.
Da yake jawabi, Gwamna Namadi ya ce sabon tsarin ya buɗe wani sabon babi na tsara ci gaba cikin tsari, tare da sanya muradun al’umma da sahihan bayanai a gaba wajen gudanar da mulki a ƙananan hukumomi.
Ya tuna cewa a baya an taɓa aiwatar da wasu tsare-tsaren bunƙasa ƙananan hukumomi irin su LEEDS, sai dai ba su samu dorewa ba saboda rashin haɗa su da kasafin kuɗi da kuma aiwatar da su yadda ya kamata.
A cewarsa, sabbin tsare-tsaren da aka ƙaddamar sun kasance wani yunƙuri na farfaɗo da inganta tsarin tsara ci gaba, inda kowace ƙaramar hukuma ta samu cikakken shirin shekaru biyar da zai jagoranci fifikon ayyuka, zuba jari da inganta ayyukan yi wa al’umma hidima.
Gwamnan ya bayyana cewa an daidaita tsare-tsaren da Ajandar Gwamnatinsa mai Maki 12, Tsarin Bunƙasa Jihar Jigawa da kuma Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDGs).
Ya ƙara da cewa an samar da tsare-tsaren ne bayan tattaunawa da shawarwari masu faɗi da suka haɗa da ma’aikatun gwamnati, ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya da na addini, mata, matasa, masu nakasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran al’umma.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa nasarar shirin za ta ta’allaka ne kan yadda za a aiwatar da shi.
“Ba ma son waɗannan tsare-tsare su kasance takardu da za a ajiye a kan shelbi. Dole ne su zama ginshiƙin tsara kasafi, aiwatar da ayyuka, sa ido da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana,” in ji shi.
Saboda haka ya umarci dukkan ƙananan hukumomi 27 da su riƙa amfani da tsare-tsaren a matsayin jagora wajen shirya kasafin kuɗi, ayyuka da shirye-shiryensu na ci gaba.
Ya kuma yi kira ga abokan hulɗar ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu, sarakunan gargajiya da na addini da sauran al’umma su mara wa aiwatar da tsare-tsaren baya domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Tun da farko, Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Raya Al’umma ya bayyana cewa ƙaddamar da tsare-tsaren wani muhimmin mataki ne na cika burin gwamnatin Namadi na samar da shugabanci nagari da bunƙasa al’umma ta hanyar tsare-tsare masu inganci.
Ya ce an tsara tsare-tsaren ne bayan shawarwari da ma’aikatun gwamnati, ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, mata, matasa, masu nakasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, wannan ne karo na farko da kowace ƙaramar hukuma a Jigawa ta samu cikakken tsarin bunƙasa na shekaru biyar wanda ya dace da manufofin ci gaban jihar, na ƙasa da kuma na duniya.
Kwamishinan ya bayyana cewa tsare-tsaren za su zama jagora wajen tsara kasafin kuɗi, zaɓen ayyukan raya ƙasa, sa ido da tantance nasarorin da aka samu.
Ya kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su rungumi tsare-tsaren tare da haɗa su cikin kasafinsu da shirye-shiryensu na ci gaba.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) reshen Jigawa kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutse, Dr. Sibu Abdullahi, ya yabawa Gwamna Namadi bisa abin da ya kira gagarumin tarihin da ya kafa.
Ya ce wannan ne karo na farko cikin fiye da shekaru 30 da dukkan ƙananan hukumomin jihar suka samu cikakken tsarin bunƙasa na shekaru biyar.
Dr. Sibu ya ce tsare-tsaren za su taimaka wajen tsara ayyukan raya ƙasa, inganta hidimomin jama’a, jawo zuba jari da kuma tabbatar da ci gaba mai ma’ana.
Ya tabbatar da cewa shugabannin ƙananan hukumomi 27 sun ɗauki alƙawarin aiwatar da tsare-tsaren ta hanyar haɗa su cikin kasafin kuɗi da shirye-shiryensu na ci gaba.
Ya ce, “Aikinmu na ainihi ya fara ne daga yau. Za mu tabbatar da cewa waɗannan tsare-tsare sun zama kayan aiki na gaskiya wajen kawo sauyi da inganta rayuwar al’ummar ƙananan hukumominmu.”
A ƙarshe, ya gode wa Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Raya Al’umma, kwamitocin fasaha, masu ba da shawara, abokan hulɗar ci gaba, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da duk waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen kammala wannan muhimmin aiki.
Ana sa ran Tsare-tsaren Bunƙasa Ƙananan Hukumomin na 2025–2030 za su zama tubalin da zai jagoranci ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a matakin ƙasa, tare da ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da ingantaccen shugabanci a faɗin Jihar Jigawa.