Dokta Lawan Ahmed Muhammad Sani ya zama sabon Sarkin Gumel

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Dokta Lawan Ahmed Muhammad Sani, a matsayin sabon Sarkin Gumel.

Dokta Lawan ya zama Sarki na 17 a tarihin masarautar Gumel.

Dokta Lawan ya gaji mahaifinsa, marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani II, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba 2026, bayan ya shafe shekaru 46 yana mulkin masarautar.

Sakataren Gwamnatin Jigawa, Bala Ibrahim, ya ce naɗin sabon Sarkin ya biyo bayan shawarar masu zaɓen Sarki na Masarautar Gumel da Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa.

Kafin naɗinsa, Dokta Lawan yana riƙe da Sarautar Chiroman Gumel, sannan yana aiki a matsayin Daraktan Tsaron Fasahar Sadarwa (Cyber Security) a NITDA.

Aƙalla mutane tara ne suka nemi kujerar Sarautar Gumel, kafin a zaɓi Dokta Lawan a matsayin sabon Sarkin.

Gwamna Namadi ya taya sabon Sarkin murna tare da yi masa fatan samun nasara wajen jagorantar al’ummar Masarautar Gumel.

Gwamnatin Jigawa ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayi Sarkin Gumel da al’ummar masarautar, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa,.

 

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu