• Home  
  • Jihar Bauchi Ta Samu Tallafin Riga-kafin Cutar Folio Daga UNICEF
- Babban Labari - Lafiya

Jihar Bauchi Ta Samu Tallafin Riga-kafin Cutar Folio Daga UNICEF

Asusun tallafa wa ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ya ba da tallafin maganin rigakafin foliyo na ɗigawa a baki guda miliyan biyu da rabi 2.5 a jihar Bauchi. Babban jami’in UNICEF da ke Bauchi, Nuzhat Rafique, ce ta miƙa waɗannan magunguna da aka ajiye su a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) […]

Asusun tallafa wa ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ya ba da tallafin maganin rigakafin foliyo na ɗigawa a baki guda miliyan biyu da rabi 2.5 a jihar Bauchi.

Babban jami’in UNICEF da ke Bauchi, Nuzhat Rafique, ce ta miƙa waɗannan magunguna da aka ajiye su a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi.

Mis Rafique ta ce za a gudanar da rigakafin ne a faɗin jihar a ranar 24-29 ga watan Afirilu.

Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbata sun wayar da kan al’umma game da wannan shiri na allurar rigakafin domin yi wa yara masu yawa a jihar.

A cewarta jihar Bauchi na daga cikin jihohin da ake da yaran da ba a taɓa yi musu rigakafin allurar foliyo ba. Jihar na da kananan hukumomi 20 kuma 13 daga ciki suna fama da wannan matsala.

“Akwai kusan yara 556,000 da ake da su a jihar da ba a taɓa yi musu allurar rigakafi ba a jihar.”

“Za mu fara da waɗannan ƙananan hukumomi a ranar 24 ga watan Afirilu kuma muna roƙon da a yaɗa wannan labari ga al’ummar da wannan abu ya shafa.”

“Muna fatan yi wa kowanne yaro da yake ƙasa da shekara 5 domin rage adadin yara 556,000 da ake da su a jihar.”

Mahukuntan UNICEF sun roƙi al’umma da su ba da haɗin kai ta hanyar zuwa cibiyoyin da za a yi rigakafin a duk inda jami’an asusun suka shirya zuwa.

Ta kuma jaddada muhimmanncin wannan allura ga rayuwar yara da ma waɗanda za su zo a bayansu.

Haka kuma babban jami’in lafiya na UNICEF a jihar Bauchi, Patrick Akor, ya bayyana cewa, UNICEF za ta samar da alƙalamin da za a yi wa yaran da aka yi wa ɗigon maganin alama tare da tabbatar da cewa kowacce ƙaramar hukuma tana da wadataccen maganin.

Bappah Jika, wanda ke wakiltar hukumar lafiya a matakin farko a jihar Bauchi, ya tabbatar da samun waɗannan magunguna daga asusun UNICEF wanda ya nuna godiyarsa ga ƙoƙarin ceton rayukan al’umma da suke yi.

Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin sanƙarau fiye da kwalba miliyan ɗaya daga asusun yaƙi da cutar a ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka tare da tallafin cibiyar samar da rigakafi ta GAVI  a ranar Juma’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000