Home » Jihar Lagos:’Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɗan Ƙungiyar Biafra

Jihar Lagos:’Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɗan Ƙungiyar Biafra

by Anas Dansalma
0 comment

‘Yan Sanda a jihar lagos sun kame shugaban kungiyar ‘Yan kabilar Igbo da ke yankin Ajao Estate a jihar Lagos bisa ikirarin gayyato ‘yan Ƙungiyar kabilar Igbo masu ikrarin kafa kasar Biafra wato IPOB zuwa garin na Lagos. 

Mutumin mai suna Fredrick Nwajagu ya yi magana ne a cikin wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sa da zumunta, inda yake cewa za su gayyato ‘ya’yan ƙungiyar ta IPOB domin su kare musu kantinansu, yana mai cewar lallai za su biya su kuma za su shirya hakan domin a daina kai musu farmaki dare da rana.

Nwajagu ya ce a da dai suna da tsaro amma yanzu sun fahinci dole sai sun gayyato matasa ‘yan kabilarsu domin su ba su tsaron da ya kamata.

Wata majiya daga hukumar ‘yan sandan da ta nemi a saka ya sunanta ta ce, hadin guiwar jami’an ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan da na farin kaya ne suka kama shugaban ‘yan kabilar ta IGBO.

Majiyar ta kara da cewar jami’an sun je gidan mutumin da fari inda ya tsere amma daga bisani suka gano inda ya buya kuma suka kama shi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi