Home » Wani Ɗan Jarida Ya Rasa Ransa

Wani Ɗan Jarida Ya Rasa Ransa

OYO/Mutuwar Wani Dan Jarida

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Wani ɗan jarida mai gabatarwa a gidan rediyo mai suna Baba Bintin ya yanke jiki ya faɗi a hanyarsa ta zuwa aiki a safiyar ranar Asabar ɗin.

Majiyarmu ta rawaito cewa ɗan jaridar yana aiki ne da gidan rediyon Fresh FM, kuma shi ne mai gabatar da wani shiri kan harkar kasuwanci a faɗin jihar ta Oyo.

Majiyarmu ta raiwito cewa wannan abin alhini ya faru ne a daidai lokacin da marigayin ya fito daga gida da zummar zuwa wurin aiki daga unguwar Amuloko inda yake zaune tare da daɓawa a ƙasa saboda rashin samun takardar kuɗin da zai biya kudin mota zuwa wurin aikinsa.

Kwatsam yana tafiya sai kawai ya yanke jiki ya faɗi nan da nan aka kira wurin aikinsa, sai dai ba jimawa rai yai halinsa.

Ƙarancin takardun kuɗi na cigaba ta’azzara tun bayan sake fasalin kudi na naira 200 da 500 da 100 wanda hakan in za a iya tunawa ya tilasta wa wasu gwamnoni kai ƙararar babban  bankin ƙasa.

Sai dai duk da hukuncin kotu na kwana-kwanan da ta yi game da yin watsi da wannan ƙuduri na sauya fasalin takardun kudin tare da umartar babban banki da ba da umarnin cigaba da amfani da takardun kuɗi na naira 1000 da 500 baya ga 200, har izuwa yanzu dai kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Domin kuwa ko a jikin gwamnatin tarayya wajen yin biyyya ga wancan umarni na kotu.

Har izuwa yanzu dai rahotonni na nuna cewa wasu ƙananun bankuna na cigaba da ba da tsofaffin takardun kudin, sai dai su ba sa karɓa idan an zo ajiya a bankunan nasu.

Abin jira dai a ga shi ne ko sabuwar gwamnati za ta yi mi’ara-koma-baya game da wannan ƙunduri.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?