Rundunar Civil Defence a Najeriya ta ce ta yi nasarar kama gangar man fetur 150 da aka yi safarsa da niyyar fitarwa daga ƙasar nan zuwa ƙasar Kamaru tare da wasu mutum biyu da ake zargi.
Babban kwamandan hukumar a jihar Akwa Ibom Yusuf Imam ne ya bayyana hakan a yau ga manema labarai a Oyo babban birnin jihar.
Imam ya ce sashen rundunar mai kula da gaɓar teku ne ya yi aiki da bayanan sirrin da ya samu na cewa wasu mutane ɗauke da man fetur a cikin kwale-kwalen katako na kan hanyar zuwa Kamaru.
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun kuma ƙwace injina biyar tare da wani inji da ake amfani da shi wajen satar mai.
Imam ya kuma ƙara jan kunnen masu aikata irin waɗananna laifuka a gabar ruwa waɗanda ke yin ƙafar-ungulu ga tattalin arzikin ƙasar nan da cewa za su fuskanci mummunan hukunci.