• Home  
  • Jirgin Kasa Dauke Da Fasinjoji Ya Yi Hatsari A Hanyar Kaduna-Abuja
- Babban Labari - Labarai

Jirgin Kasa Dauke Da Fasinjoji Ya Yi Hatsari A Hanyar Kaduna-Abuja

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya faɗi a ranar Talata da safe. Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin. Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa […]

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya faɗi a ranar Talata da safe.

Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma jirgin ƙasa ta bar Abuja ne da misalin karfe 9:45.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000