• Home  
  • An Kama Yan Bindiga 5 A Jihar Kebbi
- Babban Labari - Labarai

An Kama Yan Bindiga 5 A Jihar Kebbi

’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa […]

’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi.

Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya.

Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara.

Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai