• Home  
  • KACRAN ta buƙaci manoma da makiya su zauna lafiya
- Babban Labari

KACRAN ta buƙaci manoma da makiya su zauna lafiya

Ƙungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta yi kira ga manoma da makiya da su girmama ta hanyar kiyaye tsakanin gonaki da gandun daji da burtulai da aka ware domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar baki ɗaya. KACRAN ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta […]

Ƙungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta yi kira ga manoma da makiya da su girmama ta hanyar kiyaye tsakanin gonaki da gandun daji da burtulai da aka ware domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar baki ɗaya.

KACRAN ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannu Khalil Moh’d Bello, inda ta ce a shirye take ta cigaba da shigewa gaba domin samar da hanyoyin da za a zauna lafiya tsakanin manoma da makiya.

“Daminar bana ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya. Wannan ya sa a matsayinmu na ƙungiya mai son zaman lafiya muke ta ƙoƙarin ganin mun wayar da kan mutane muhimman zaman lafiya,” in ji shi.

Ƙungiyar ta ce daga cikin hanyoyin da za a bi domin inganta zaman lafiya akwai girmama juna, inda ta ce akwai buƙatar, “manoma su guji cinye burtalai, sannan makiyaya su guji shiga gonaki,” in ji ta, sannan ta ce hakan zai samar da zaman lafiya, sannan manoma su yi noma ƙasar ta samu abinci.

A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su samar wa manoma da kayan noma cikin rahusa, sannan a ƙwato tare da sake mayar da gandun daji domin makiyaya su samu wurin kiwon dabbobinsu ba tare da shiga gonakin manoma ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000