Dakarun Sojin Najeriya, sun kama Kachalla Halilu wanda ake zargin ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindiga ne a Jihar Zamfara.
An kuma gano wasu kayayyaki a wajensa da suka haɗa da babur, wayar salula, hula da kuma wasu magungunan dabbobi.
Wata majiya ta ce nasarar kamen ta samu ne saboda yadda sojojin suka yi aiki da bayanan sirrin da suka samu cikin gaggawa.
Bayan kama shi, an miƙa wanda ake zargin ga jami’an leƙen asiri domin ci gaba da bincike da gano irin rawar da ya taka a hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Kamen na daga cikin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Jami’an tsaro sun ce binciken da ake yi zai taimaka wajen gano ƙarin bayanai kan ayyukan ta’addanci da wanda ake zargin ke da hannu a ciki.
