Kamfanin Google ya karrama dan kwallon kafar Najeriya

Kamfanin Google ya karrama marigayi dan kwallon Najeriya, Rashidi Yekini ta hanyar sanya zanensa a shafin na google a daidai lokacin da dan wasan ke cika shekaru 60 da haihuwa.

BBC ta rubuta cewa Yekini dai ya faɗa ƙangin talauci da rashin matsuguni bayan yin fice a matsayin ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na Najeriya.

Zanen na Google ya kwatanta murnar da Yekini ya yi lokacin da ya ci wa Najeriya ƙwallonta ta farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

Hakan ya nuna lokacin da Yekini ya zura ƙwallo a ragar Bulgeriya, ya shige cikin ragar tare da kama ta da hannu bibbiyu yayin da hawayen murna ke kwararo masa.

Post masu alaƙa

Shugaban Hukumar kwallon Ƙafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya yi murabus

Man City ta dage kan Enzo Fernandez, Sao Paulo da West Ham na neman Vardy

Mahaifin Lionel Messi, Jorge, ya rasu yana da shekara 68