Iran ta zargi Amurka da hana jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar

Iran ta zargi Amurka da hana wasu muhimman jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar, bayan ta amince wa ‘yan wasan da wasu ma’aikatan tawagar bizar halartar Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Iran ta ce an ƙi bai wa da dama daga cikin jami’an gudanarwa da masu ba da shawara biza, lamarin da ofishin jakadancinta da ke Turkiyya ya bayyana a matsayin tsoma baki a harkokin wasanni saboda dalilai na siyasa.

Sai dai Amurka ta ce ta bai wa ‘yan wasan da ma’aikatan da ake buƙata biza, tare da jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da tsarin gasar wajen shigar da mutanen da ake zargi da alaƙa da ta’addanci ba.

Iran ta kuma yi kira ga FIFA da ta shiga cikin lamarin, yayin da rahotanni daga Iran suka ce shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar da mataimakinsa na cikin waɗanda aka hana shiga Amurka.

A makon nan, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce ba za a amince da mutanen da ke da alaƙa da dakarun IRGC su shiga cikin tawagar ƙwallon ƙafar Iran ba.

Iran za ta buga wasanta na farko a gasar da za a yi a Amurka da Canada da Mexico ranar 15 ga Yuni a Los Angeles.

Post masu alaƙa

Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Galadima ya rasu

Senegal ta lashe gasar AFCON ta 2025