Home » Kananan Yara Sama Da Miliyan 1 Za Su Rasa Tallafin USAID

Kananan Yara Sama Da Miliyan 1 Za Su Rasa Tallafin USAID

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yara miliyan ɗaya da dubu ɗari uku, ƴan ƙasa da shekara biyar masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki ne ke fuskantar barazanar daina samun tallafi a ƙasashen Habasha da Najeriya.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yara miliyan ɗaya da dubu ɗari uku, ƴan ƙasa da shekara biyar masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki ne ke fuskantar barazanar daina samun tallafi a ƙasashen Habasha da Najeriya.

UNICEF ya ce nan da watanni biyu abinci mai gina jiki da sauran magungunan da yake amfani da su wajen yaƙi da lalurar a ƙasashen biyu za su ƙare saboda rashin masu ɗaukar nauyi.

Lamarin na da alaƙa da matakin shugaban Amurka, Donald Trump na rage tallafin da Amurkan ke bai wa ƙasashen waje.

Mataimakiyar shugabar Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Kitty Van der Hayden, a yayin wani taron manema labarai a jiya Juma’a, ta ce katsewar masu ɗaukar nauyin ayyukan nasu zata mayar da hannun agogo baya a kan nasarorin da UNICEF ya samu wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin sheakaru 25.

Ta ce “Mun yi ƙiyasin cewa idan har ba a samu sabbin waɗanda za su ɗauki nauyin aikin ba daga yanzu zuwa watan Mayu, UNICEF za ta gaza samar da magungunan kula da ƙananan yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki da yawan su ya kai 74,500 a ƙasar Habasha.”

Ta ƙara da cewa “A Najeriya ma, inda ƙananan yara aƙalla 80,000 ke ƙarɓar maganin wannan ciwo a kowanne wata, magungunanmu za su ƙare daga wannan watan zuwa ƙarshen Mayu.”

A watan Janairun bana shugaba Trump na Amurka ya dakatar da ayyukan hukumar USAID mai bayar da tallafi ga ƙasashen duniya, a wani mataki na rage kuɗaɗen da ƙasar ke kashewa wajen ayyukan tallafi.

Matakin wanda Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi da ƙungiyoyi suka yi allawadai da shi, ya jefa fargaba a tsakanin ƙasashe masu tasowa, musamman a nahiyar Afirka, inda ake dogaro da irin ayyukan da USAID ke gudanarwa wajen aiwatar da muhimman abubuwan ci gaba.

USAID ta kasance kan gaba wajen gudanar da ayyukan tallafi a Afirka, inda ta shafe fiye da shekara 30 tana ɗaukar nauyin shiryen-shiryen yaƙi da cutukan da suka addabi jama’a, kamar zazzaɓin cizon sauro da HIV/AIDS da tarin fuka da dai sauran su

UNCEF ya ce dakatar da tallafin Amurkan ya kuma shafi aikin yaƙi da cutuka masu damun mata masu juna biyu da kuma jarirai, a Habasha, inda tilas aka rufe wasu cibiyoyin kula da lafiyar jama’a.

A Najeriya, akwai ƙananan yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, musamman a yankin Arewa masu Gabashin ƙasar, inda ake fama da rashin tsaro, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilastawa wasu miliyoyi barin muhallin su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?