Home » An Kama ‘Yan Daba 12 Kan Zargin Kashe Matashi A Masallaci A Kaduna

An Kama ‘Yan Daba 12 Kan Zargin Kashe Matashi A Masallaci A Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar kama wasu ‘yan daba  12, da ake zargin sun kashe wani matashi ana tsaka da sallar Tahajjud a Kaduna.

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu ‘yan daba  12, da ake zargin sun kashe wani matashi ana tsaka da sallar Tahajjud a Kaduna.

Wasu da ake zaton ‘yan daba ne sun kai wa wani matashi hari a masallacin Rigasa a Jihar Kaduna, inda suka kashe shi ana tsaka da sallar Tahajjud.

Rundunar ‘yan sandan jihar sun samu nasarar kama mutum 12 da ake garin da sa hannunsu a kai hari masallacin.

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, yace ‘ ‘yan daban sun fito daga unguwanni daban-daban kamar Malalin gabas, Tudun wada, Rafin guza, da Unguwar Baduko’.

Sun kai farmakin ne a Masalllacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalign karfe 2 na dare.

Kafin jami’an tsaro sukai wajen, tuni ‘yan daban sun cakawa matashin Usman Muhammad, mai shekaru 28 wuka har lahira.

Rundunar tarer da hadin gwiwar JTF sun dauki mataki cikin gaggawa, inda suka kama mutum 12 kuma ana bincike a kansu.

Inda aka samu makamai a hannunsu.

An fara bincike domin gano gaskiyar lamarin da tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata lifin.

‘Yan sanda sun kara tsaurara matakan tsaro a wureren da ake gudanar da ibada, da kuma sauran wuraren da ake ganin zasu iya fuskantar barazana
Hukumomi sun bukaci al’umma da su kasance masu Sanya ido tare da gaggauta kai rahoto idan sun ga wani abun zagi.

‘Yan sandan sun kuma gargadi masu aikata laifi da su daina ko su fuskanci hukunci mai tsanani

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?