Rahotanni na cewa sojojin Sudan a ranar Asabar sun kwace wasu muhimman gine-gine a tsakiyar birnin Khartoum, ciki har da babban bankin kasar daga hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF), bayan sake ƙwace fadar shugaban kasar.
Kakakin rundunar sojin Sudan Nabil Abdallah a wata sanarwa da ya aika wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce, “Dakarunmu sun samu ƙarin nasara a daren jiya, inda suka kawar da ɗaruruwan ‘yan bindiga da suka yi ƙoƙarin tserewa a tsakiyar birnin Khartoum,” inda ya lissafa gine-ginen da aka kwato ciki har da babban bankin kasar.
Sojojin ƙasar da ƙawayensu masu ɗauke da makamai sun sake ƙwace fadar shugaban kasar a ranar Juma’a daga hannun dakarun RSF, inda ƙungiyar ta RSF ta yi ramuwar gayya ta hanyar kai hari da jiragin yaƙi mara matuki suka kashe ‘yan jarida uku da wasu sojojin kasar.
- Wadan Da Suka Ci Zarafin Yarinya A Kan Mangwaro Basu Ci Bulus Ba— Zulum
- Wuyar Da Na Sha A Gidan Yari Ce Ta Sanya Zan Koma Yin Wa’azi A TikTok: Ummin Mama
A ranar Juma’a, majiyoyin soji sun ce mayaƙan na RSF sun tsere zuwa cikin gine-gine a Al-Mogran, wani yanki da ke yammacin fadar da ke da bankuna da kuma hedkwatar kasuwanci. Dakarun na RSF sun sanya ƙwararrun masu harbin bindiga a gundumomi da ke da tsauni, wadanda ke sa ido a Omdurman da ke gabar kogin Nilu da ma’aikatun tsakiyar birnin Khartoum.
Yaƙin da ake yi na neman iko da gwamnatin Sudan da kuma samun gundumomin da ake hada-hadar kuɗi a Khartoum zai iya sa sojojin ƙasar su samu ƙarin iko da babban birnin.
Tun daga watan Afrilun 2023, sojoji ƙarƙashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan ke yaƙi da RSF, ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin kwamandan Burhan wato Mohamed Hamdan Daglo.
Yakin ya kashe dubban mutane, ya raba fiye da mutum miliyan 12 da muhallansu tare da haifar da matsalar yunwa. Kazalika rikicin ya raba kasar gida biyu, inda sojoji ke rike da gabas da arewa yayin da RSF ke iko da kusan daukacin yankin yammacin Darfur da wasu sassan kudu. Kamar yadda kafar yada labarai ta TRT ta wallafa.