Home » Najeriya Ta Fara Shirin Kwaso Dalibanta Da Ke Sudan -Mr. Jeoferry Onyeama

Najeriya Ta Fara Shirin Kwaso Dalibanta Da Ke Sudan -Mr. Jeoferry Onyeama

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnatin Najeriya Za Ta Fara Kwaso ‘Yan Kasar nan da suka Makale a ƙasar Sudan, biyo bayan yaƙin da ya ɓarke wanda hakan ya sanya dubban ɗaliban ƙasar nan cikin tsaka mai wuya.

Ministan Harkokin wajen Najeriya Mr. Jeoferry Onyeama ne ya ba da tabbacin cewa daga yau zuwa gobe Najeriya zata fara kwaso ‘yan kasarta daga Sudan inda rikicin cikin gida ke ci gaba da kara tsananta. Ministan ya ce suna jiran sahalewar gwamnatin Sudan ne da nufin fara kai ‘yan Najeriya zuwa makwabciya, kasar Masar, daga inda za a yi jigilar su domin dawo da su gida Najariya.
Ya kuma kara da cewa, tuni aka fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin Najeirya da ke Masar da Sudan domin tsara yadda za a yi jigilar. A daidai lokacin da Amurka ta yi amfani da jiragen yaki domin kwashe jami’an difflomassiyarta sama da dari daga birnin Khartoum su ma kasashe irin su Faransa, Jamus da dai sauran kasashe, tuni suka yi nisa wurin kwashe mutanensu dake kasar ta Sudan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?