Ƙungiyar likitoci musulmai na kasa ta kai tallafin kayan more rayuwa ga ɗaurarrun mutane dake gidajen gyaran hali na gwauron Dutse da Kurmawa
Shugaban kungiyar na jihar kano Dr Muhammad Auwal ya ce, suna yin aikin ne dan taimakawa marasa karfi a wurare daban daban, tare da basu kayan abinci da ruwa da makamantan su.
DA yake jawabinsa shima Dr Anas Ibrahim Yahaya bichi wanda yana cikin tawagar likitocin da suka duba marasa lafiyar yace babu kalar likitocin da babu a cikin su
Dr Muhd Lawan Adamu ya ce ko wace irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta
Daga karshe maimkula da gidan gyaran halin na kurmawa DC Mu’Azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugabanhukumar ya nuna godiya da jin dadin su kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.