A gudanar da makon Kimiyya da Fasaha da murnar ranar Kimiyya da Fasaha ta Duniya wanda aka yi a dakin taro na coronation hall da ke gidan gwamnatin jihar nan.
Hukumar Kimiyya da Fasaha da Kirkire-kirkire ta Kano ce ta shirya wannan mako wanda ya kunshi gasar kaci-kaci na kimiyya da fasaha wanda kuma aka raba wa daliban da suka yi nasara kyautattu.
A wurin taron mokon kimiyya da fasaha wanda aka shirya domin ranar Kimiyya da Fasaha ta Duniya, an gudanar da abubuwa da dama da suka hada da: ba da kyaututtuka ga daliban da suka yi nasara daga makarantu daban-daban da suka shiga gasar kaci-kaci domin nuna basira da Allah ya ba su a wannan fanni.
Inda kuma gwamnan jihar Kano, wanda mataimakinsa, Comr. Aminu Abdusalam Gwarzo, ya wakilta, ya karrama su da kayututtuka ga wadanda suka yi nasara.
Gabanin haka, daliba makarantar Queen’s College da Musa Iliyasu College sun gabatar da wasann kwaikwayo.
A a yayin jawabinsa, mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Kano kan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Sharada ya yaba wa Gwamnan Kano game da goyon baya da yake bayarwa ga wannan ɓangare.
An kuma gabatar da Makalu game da fannin na kimiyya da fasaha, inda Dr. Aminu Bature daga Jami’ar Bayero ya gabatar da Makala game da sabuwar Fasahar Kirkirarriyar basira da aka fi sani a Turance da Artificial Intelligence.
A yayin jawabinsa, Mataimakin gwamnan jihar Kano, Comr. Aminu Abdusalam Gwarzo ya tabbatar da aniyar gwamnatin jihar Kano tare da bayyana muhimmancin Kimiyya da Fasaha ga al’ummar jihar nan.
Daga karshe ne, kwamishinan Hukumar Kimiyya da Fasaha da Kirkira, ya raba wasu muhimman baki shaidar karramawa domin yaba irin gudunmuwar da suka bayar wajen bunkasar kimiyya da fasaha a jihar Kano.