Ana cigaba da kawo muku rahotonni game da yadda zaɓe ya gudanar da yadda ake haɗa sakamako.
A nan jihar Kano, tuni Majiyarmu ta rawito mana yadda Jami’an tsaro suka yi wa shalkwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Jihar Kano kawanya da motoci masu silken.
Kuma an rufe duk wasu hanyoyin da ke kai wa ga shalkwatar.
Da fari dai an bar jami’in majiyarmu ya shi ya wuce shingen, amma daga bisani an hana shi shiga babbar kofar shiga ciki ɗakin bayyana sakamako, inda aka shaida masa sai karfe wani locaci nan gaba za a buɗe wajen domin ba su damar shiga.
Kazalika, su ma mazauna yankin sun shiga tsilla-tsilla saboda an hana su shiga gidajensu.
Zaɓen jihar Kano a matakin gwamna, ana ganin yana ɗaya daga cikin zaɓuka mafi zafi da aka gudanar a jiya Asabar.