Kano: Karin ɗalibai 150 sun tashi zuwa ƙasar India

Rukuni na hudu, ɗauke da ɗalibai 150 da gwamnatin Kano mai ci ta ɗauki nauyin karatunsu a ƙasashen waje sun tashi zuwa ƙasar India domin yin karatun digiri na biyu a fanni daban-daban.

Tallafin karatun na daya daga cikin manya-manyan alkawura da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi lokacin yakin neman zaben sa.

Tuni dai aka fara shirin inda a yau Juma’a rukuni na huɗu ya tashi zuwa kasar India daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tashin ɗaliban, Kwamishinan Ilimi mai Zurfi na jihar, Dr Yusuf Kofarmata, ya ce za su sauka a Legas ne kafin su wuce zuwa India.

A cewar sa, da saukar su a India, za a kwashe su zuwa jami’o’i daban-daban da za su yi karatun su a fannonin ilimi daban-daban.

Post masu alaƙa

Barista Hamza Ɗantani ya jinjinawa CP Bakori da wasu kwamishinonin yan sanda biyu.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.

Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai