Home » Kano: Kungiyar Ma’aikatan Jinya Ta Koka Kan Hana Likitoci Fita Ƙasashen Ƙetare

Kano: Kungiyar Ma’aikatan Jinya Ta Koka Kan Hana Likitoci Fita Ƙasashen Ƙetare

by Anas Dansalma
0 comment
Kano: Kungiyar Ma'aikatan Jinya Ta Koka Kan Hana Likitoci Fita Ƙasashen Ƙetare

Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta kasa (NANNM) reshan Jihar Kano, Kwamred Ibrahim Maikarfi Muhammad ya bayyana cewa hana likitoci fita wajen Nijeriya danyaen aiki ne, domin a nan gida Nijeriya ba a ba su hakkinsu yadda ya dace.

Kwamred Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci kan yunkurin hana likitocin Nijeriya fita kasashen ketare da cefanar da asibitoci a wata hira da manema labarai suka yi da shi a ranar Alhamis a ofishin kungiyar NANNM da ke Kano.

Haka kuma ya bayana kalubale uku da za a duba wajen warware matsalar korafe- korafe a asibitocin da ake samu yau da kullum, na farko akwai laifin hukuma na karacin ma’aikata da kayan aiki, sannan rashin samun cikakaken horo daga wasu ma’aikatan lafiyar ko rashin tarbiya na wasu ma’aikatan lafiyar ga kuma cinkoson aiki a asibutocin.


Ya ce akwai matsalar mutane na rashin fahimta ko hakuri wajen neman lafiya wanda suna bukatar kyakyawar fadakarwa daga hukuma na sanin hakin ma’aikacin lafiya da kuma hakinsu na masu neman lafiya ta yadda kowa zai kiyaye doka da ta hau kansa da dai sauransu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?