Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ahmadu Haruna Zago, yace hukumar sa za ta yi amfani da sashen dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da ba su kamata ba a jihar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai yayin da ma’aikatan hukumar suke tsaka da aikin kwashe sharar dake fagge, ‘yan Alluna.
Dan zago yace abin takaici ne yadda wasu suke bin tsakar dare suna jibge shara akan titunan jihar nan da wuraren da basu dace ba, musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.
A bayanansu tunda farko mazauna kasuwar ta Fagge ‘yan Alluna, sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan, Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa ya kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.