An yi kira ga masu sana’ar kira da su kiyaye nau’in mutanen da za su siyar wa da kayan kirarsu musamman makamai na hannu duba da halin rashin tsaro da ake fama dashi.
Kwammishiann Yan Sandar jahar Kano Muahammad Husaini Gumel ne ya yi wanan kira yayin da yake holon masu laifi sama da 90 da rundunar ta cafke.
Sama da masu laifi 90 ne rundunar yan sadar jahar kano tayi nasarar chafkewa a fadin jahar.
Masu laifin sun hada yan satar mutane da garkuwa da su, yan fashi da makami, yan daba da barayin ababan hawa da dai sauran su.
Da yake holon su a shelkwatar hukumar Yan Sanda dake Bompai a nan jahar Kano, CP Muhammad Husaini Gumel ya ce jan hankali masu sana’ar kira ya zama wajibe su yi nazarin masu sayen hajarsu, duba da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar nan baki daya.
Kwamishinan ya bayyana cewar duk makerin da aka samu yana siyarwa da yan fashi makamai lallai zai fuskanci fushinn hukuma domin ba sani ba sabo.
Cp Muhammad Husani Gumel ya bayyana yadda aka bin ciko wata mota mai tsada da aka sace daga nan kano kuma aka kaita wasu kasashen makwabta.
Kwamshunan ya yabawa al’umar jahar kano bisa irin hadin kan da su ke bawa yan sanda da sauran jami an tsaro wajen kokarinsu na dakile masu aikata laifuka musamman a kwaryar birnin Kano.