Home » Kano:An Harbe Wani Kantsila Kan Zargin Satar Akwati

Kano:An Harbe Wani Kantsila Kan Zargin Satar Akwati

Zaɓen Gwamnoni da 'Yan Majalisu

by Anas Dansalma
0 comment

Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar ɗin nan.

Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa a Getso.

Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara.

Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.Ita ma a na ta ɓangaren, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi