Home » Kasar Rasha ta yi alkawarin karasa kera wa Najeriya jiragen yaki 12

Kasar Rasha ta yi alkawarin karasa kera wa Najeriya jiragen yaki 12

by Anas Dansalma
0 comment
Kasar Rasha ta yi alkawarin karasa kera wa Najeriya jiragen yaki 12

Rasha na son kammala samar da jiragen yaƙi masu saukar ungulu na Mi-35 guda goma sha biyu ga Najeriya, kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, Rian, a wajen taron Rasha da Afirka da ke gudana a birnin St Petersburg.

Dmitry Shugaev, shugaban ma’aikatar tarayya ta Rasha kan fasahar aikin soji, ya ce yarjejeniyar sojan ita ce za ta taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar kungiyoyin ƴan ta’adda da kuma shigar da ƙasar cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Sai dai bai bayyana adadin jiragen yaƙin da aka kawo ba izuwa yanzu ko kuma lokacin da za a kammala kawo sauran jiragen ba, amma ya ce ƙasar na da sha’awar kammala jigilar jiragen nan ba da daɗewa ba.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce Najeriya za ta haɗa gwuiwa da ƙasar Rasha domin farfaɗo da kamfanin sarrafa aluminium na ƙasar nan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?