A gobe Lahadi shugabannin Yammacin Afrika za su gudanar da wani taron gaggawa don tattaunawa kan juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kuma sabon shugaban kungiyar ta ECOWAS, shi ne zai jagoranci zaman na ranar Lahadi wanda za a yi a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da juyin mulkin a cikin wata sanarwa inda kuma ya yi wa al’ummomin kasashen waje alƙawarin cewa zai yi iyakacin ƙoƙarinsa domin kare dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da ɗorewar kyakkyawan shugabanci a yankin.