Likitocin asibitocin gwamnatin tarayyar ƙasar nan sun fara yajin aikin sai baba ta gani bisa zargin gwamnati da gazawa wajan magance matsalolinsu.
Likitocin dai na buƙatar gwamnati da ta biya su dukkan albashinsu da kuma alawus alawus din da ya kamata a basu.
Kungiyar likitoci ta ƙasa ta ce akalla likitoci 50 na barin ƙasar nan a kowanne mako inda suke fita kasashen waje don su yi aiki a can.
Rashin biyan likitoci albashi mai kyau da rashin cikakkun kayan aiki a asibitoci da ma tsadar rayuwa na daga cikin abubuwan da ke sa likitoci fita daga kasar nan don neman aiki a waje.
Yajin aikin likitoci a ƙasar nan na shafar ayyukan lafiya musamman a asibitocin gwamnati.