Ƙasar China da Amurka sun yi tsokaci kan ci gaban da aka samu wajen amincewa su ci gaba da hulɗa a tsakaninsu bayan kwashe wasu lokuta suna zaman doya da manja.
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da manyan jami’an diplomasiyyar ƙasashen suka yi a China, ta bayyana cewa an samu ci gaba sosai a tattaunawar da ƙasashen biyu suka yi.
Daga cikin batutuwan da sanarwar mai ɗauke da sa hannun mataimakin sakataren ƙungiyar ƙasashen gabashin Asiya da na yankin pacific, ta fitar, har da batun ‘yancin ɗan adam da kuma halin da ake ciki a Taiwan.
Ya ce Amurka na kokari sosai wajen daidaita dangantakarta da China.