Gwamnatin Kano da ta shuɗe ta mayar da martani game da zargin sayar da Asibitin Asiya Bayero wanda gwamnati mai ci ta Abba Kabir Yusuf ta ce ta ƙwace a yan kwanakin nan.
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na gwamnatin Ganduje, Muhammad Garba a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, ya ce an dakatar da ayyukan asibitin Asiya Bayero ne wani ɗan lokaci ne bayan kammala aikin asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu.
Ya ce sabon asibitin ƙananan yaran wanda ya fi wancan yawan gadaje, a yanzu yana samar da ingantattun ayyuka baya ga cibiyar horar da ma’aikata da kuma ayyukan bincike da ke ciki.
Muhammad ya yi nuni da cewar an yi shawarar mayar da tsohon asibitin Hasiya Bayero zuwa cibiyar kula da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da aka fi sani da tamowa, wanda zai zama cibiyar kula da cutar.
Kwamishinan ya ce, har zuwa ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, ba a sayar da wurin ga wani ko wata ƙungiya ba, wurin yana nan a matsayin mallakin gwamnatin jihar Kano.