Ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea, sun bayyana cewa duk wani yunƙurin yin amfani da ƙarfin soja don dawo da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum tamkar ƙaddamar da yaƙi ne a kansu.
Ƙasashen uku sun bayyana hakan ne bayan barazanar da shugabannin ƙasashen yankin yammacin Afirka, ECOWAS, suka yi cewa za su yi amfani da ƙarfi wajen farfaɗo da tsarin dimukraɗiyya a ƙasar ta Nijar idan har jami’an sojoji suka ƙi mayar da hamɓararren shugaban kasar kan karagar mulki.
Ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea waɗanda dukansu yanzu haka suna ƙarƙashin mulkin soja, maƙwabta ne ga ƙasar Jamhuriyar Nijar, kuma dukansu Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka, ko da yake a halin da ake ciki tsakaninsu ba kare bin damo.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka gabatar shugabannin mulkin soja na ƙasashen Mali da Burkina Faso, da kuma Guinea, sun yi barazanar cewa, idan ƙungiyar ECOWAS ta shiga tsakani ta hanyar yin amfani da ƙarfin soja a Nijar, to za su kawar da ƙungiyar daga yankin ɗungurungum.