Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan wutar lantarki Mista Adebayo Adelabu, ta bayyana cewa kaso 40 na ƴan Najeriya na samun wutar lantarki ta aƙalla awa 20 a kullum.
Ministan ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da aka yi duba akan nasarorin da ma’aikatar wutar lantarki ta samu cikin wannan shekara.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ministan yace nasarorin da suka samu a sakamakon jajircewa ne. Ministan ya ƙara da cewa dole ne Najeriya ta yi ƙoƙarin samar da wuta a koda yaushe domin samun cigaban tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.
“Wannan ne yasa ƙasashe irinsu China, da ƙasashen nahiyar Turai suke kan gaba wajen haɓɓakar tattalin arziƙi” a cewar Mista Adebayo.