• Home  
  • Kisan ‘Yan Arewa A Edo: ‘Yan Sa Kai Sun Zata Ɓata Gari Ne; Fred Itua
- Babban Labari - Labarai

Kisan ‘Yan Arewa A Edo: ‘Yan Sa Kai Sun Zata Ɓata Gari Ne; Fred Itua

Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai mummunan hari kan waɗansu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya, amma binciken farko ya tabbatar da cewa ‘yan sa kan sun zata ɓata gari ne a motar da suka tare. 

Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai mummunan hari kan waɗansu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya, amma binciken farko ya tabbatar da cewa ‘yan sa kan sun zata ɓata gari ne a motar da suka tare. 

Mummunan kisan gillar da aka yi wa waɗansu matafiya ’yan Arewa 16 da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na jihar Edo na ci gaba ɗaukar hankali a faɗin Nijeriya da kewaye.

An yaɗa wasu hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta da su ke nuna waɗan su mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.

Hakazalika Hotunan bidiyon da aka yaɗa sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone baki daya.

Kawo yanzu an ce gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis, ta kuma ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kan mummunan al’amarin.

Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai harin

Sanarwar ta ambato Gwamna Monday Okpebholoce na shan alwashin hukunta “masu laifin.”

“Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na Jihar Ribas suka ratso ta garin, sai ’yan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne,” kamar yadda Fred Itua ya bayyana.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ba a harin, amma ta ce Gwamna Okpebholo ya ziyarci garin a ranar Juma’a, inda ya yi alƙawarin gano waɗanda suke da hannu domin su fuskanci hukunci.

Yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamna Okpebholo ya yaba wa shugabannin ’yan arewacin Nijeriya “bisa yadda suka kwantar da al’amarin cikin hikima” in ji sanarwar.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000